Uncategorized

Amfani da Shugabannin Al’umma Zai Taimaka Wajen Magance Rikicin Boko Haram

 

Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma CITAD, ta bayyana cewa yin amfani da shugabannin al’umma zai taka rawa sosai wajen magance rikicin boko haram da ake fama da shi a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Cibiyar ta CITAD ta ce ta gano hakan ne bayan da ta gudanar da wani bincike a yankin arewa mso gabashin arewacin ƙasar nan, inda sakamakon binciken ya nuna cewa yin amfani da shugabannin al’umma da na addinai da na matasa da kuma shugabannin ƙungiyoyin mata zai taimaka sosai wajen magance wutar rikicin da ta ke kokarin gagarar Kundila, a maimakon yin amfani da ƙarfin soji.

Babban jami’in gudanar da shirye-shirye na cibiyar ta CITAD Isah Garba ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke gudanar da wata maƙala da aka gabatar mai taken hanyoyin da za bi wajen magance ƙalubalen tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Isah Garba ya ce amfani da jami’an tsaro na sa ka kai da aka fi sani da Civilian JTF zai taimaka sosai wajen daƙile wutar rikici.

Rikicin Boko Haram dai ya ɗauki tsahon shekaru fiye da goma a yankin jihohin Maiduguri da Yobe da kuma Adamawa, inda aka samu asarar dubban rayukan al’umma da dukiyoyi ta miliyoyin Naira. Tare kuma da dubban ƴan gudun hijira.

Taron dai ya samu halarcin kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, AIG Habu Sani, wanda ya samu wakilcin mataimakin kwamishinan ƴan sanda Uzairu Muhammad, da babban kwamandan rundunar Civil defense da kuma ƙungiyoyin fararen hula daga ciki da wajen jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *