Zamu cigaba da bawa CITAD Gudunmawa daidai gwargwadon mu – Inji Sarki Rano
A cigaba da shirin da take na wayar da kan al’umma kan cin zarafin da ake wa Æ™ananan yara da mata, a yau 22 ga watan Satumba na wannan shekarar Cibiyar BunÆ™asa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma ta CITAD ta kaiwa mai martaba sarkin Rano Alh. Kabiru Muhd Inuwa ziyara a fadarsa.
Makasudin ziyarar dai itace kara karfafa gwuiwa tsakanin Cibiyar da kuma shuwagabannin al’umma ta gargajiya dan samun gudunmawa wajen ganin yaÆ™ar wannan baÆ™ar al’adar a tsakanin al’ummar.
Yayin da yake jawabi a gaban mai martaba sarki Mallam Haruna Adamu Hadejia (wanda ya wakilci Shugaban Cibiyar Mallam Y.z Ya’u) ya bayyana irin gudunmawar da masarautar rano take bawa cibiyar, sannan ya kara jaddada neman goyan baya kan ganin an yaÆ™i wannan baÆ™ar al’adar.
A nasa jawabin Maimartaba sarkin Rano Alh. Kabiru Muhd Inuwa, ya nuna jin daÉ—insa tare da nuna goyan baya kan wannan yunÆ™urin na CITAD. Ya Æ™ara da cewa “al’umma idan ta yunÆ™ura dan ganin kawo wani sauyi na abinda ke damunsu, to ya zama wajibi akansu iyayen Æ™asa su marawa yunÆ™urin baya”.
Yayin ziyarar dai Cibiyar ta gabatar da wasu daga cikin Wallafe-wallafen cibiyar ga masarautar.