Activities & Projects, AI based monitoring of harmful contents, CITAD in the News, Kano Social Influencers summit (KANSIS)

Da sabuwar fasahar sadarwa ta AI za a iya inganta zaɓe a Nijeriya – CITAD

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Cibiyar fasahar sadarwa da cigaban al’umma ta CITAD ta bayyana cewa da sabuwar fasahar AI za a iya samun ingantaccen zaɓe a ƙasar nan.

Shugaban cibiyar Mal. Yunusa Zakari Ya’u ne  ya bayyana haka yayin taron  wayar da kan matasa na waɗanda suka shahara a kafafen sada zumunta na kwana 2 mai suna Kano Social Influencers Summit da ta saba shiryawa duk shekara.

Mal. Zakari ya ƙara da cewa “A wannan karon abinda muke so mu fuskanta shi ne za a yi amfani da wannan sabuwar fasahar ta AI a gyara harkar zaɓe da kuma harkokin yadda ake gudanar da gwamnati  don a samu ingancin yadda ake gudanar da zaɓen da kuma aikin gwamnati don mutane su ci muriyarsa”

A jawabinsa gwamnan  jihar Kano  Engr. Abba Kabir Yusuf, da ya samu wakilcin mai bashi shawara na musamman kan al’amuran jiha Alh. Usman Bala ya ce  sabuwar fasahar Artificial Intelligence AI na da gagarumar gudammawa wajan inganta ayyukan jama’a, da sake fasalin harkokin zaɓe a Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, sabuwar Fasahar Artificial Intelligence AI na da ƙarfin daidaita tsarin zaɓe, da rage kurakuran ɗan Adam.

Usman Bala ya cigaba da cewa “Bayar da abubuwan da suka faru a babban zaɓen Nijeriya na 2023 wanda ya shaida yadda ake amfani da matasa masu rauni wajan tashe-tashen hankulan zaɓe da kuma cin hanci da rashawa na jami’an zaɓe.”

Sannan ya bayyanar AI a matsayin wacce ke ba da damar da za ta iya magance yawancin matsalolin tsarin da suka shafi tsarin zaɓen Najeriya a tarihi.

Taron wanda shi ne karo na 5 an fara shi ne a ranar Larabar da ta gabata a ƙarƙare shi jiya Alhamis.

Kazalika taron, ya samu halartar ɗimbin matasa da masana daga cibiyoyi da jami’o’in gida Nijeriya da ƙasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *