Cibiyar Yada Fasahar Zamani da Ci gaban l’umma, CITAD, tare da hadin gwiwar Cibiyar Raya Al’adun Birtaniya a Najeriya sun yi kiran da a lalubo wasu hanyoyin na daban da matakan soji wajen kawo karshen yaki da Boko Haram – wanda ke neman kai wankin hula ya kai dare.
Cibiyoyin biyu sun tara masana da kwararru masu nazari domin lalubo dabarun da suke ganin in an yi amfani da su za a kawo karshen balahirar Boko Haram din da ta share shekara 10 ana fama da ita a Najeriya.
Babban Daraktan CITAD a Najeriya Dokta YZ Yau ya bayyanawa Aminiya cewa, masanan sun nuna amfani da karfin soji kawai ba zai kawo karshen lamarin ba, inda ya nunar dace wa sun hango cewa lokaci ya yi da dukkanin bangarori a batun su lalubo matakan da suka dace, da wadanda ba su dace ba wajen yakin da ake yi.
Kuma hakan zai sa a gano dalilan da suke sanya aka yi ta bata kashi tsakanin bangarorin biyu a baya.