COVID-19

Cibiyar CITAD ta Horas Da Matasa Guda 100 Akan Hanyoyin Kariya Daga Cutar Korona

A kokarinta na ganinta ta dakile yaduwar cutar korona a fadin kasar nan, cibiyar bunkasa fasahar sadarwa ta zamani da ci gaban al’umma CITAD tare da tallafin gidauniyar MacArthur da kuma hadin gwiwar cibiyar ilimi ta ƙasa da ƙasa wato International Institute of Education (IEE) sun horar da matasa guda 100 a jihar Kano, akan yadda za a dakile bazuwar cutar ta korona.

Taron horaswar wanda ya gudana a dandalin intanet na Zoom ya dauki tsahon kwanaki goma sha daya.

Jami’in yaɗa labarai na cibiyar CITAD, Malam Ali Sabo ya bayyana cewa an gudanar da taron da nufin wayar da kan matasa akan yadda za su dakile yaduwar korona tare da tallafawa al’umma wajen ganin an samu takaitar cutar ta korona.

Malam Ali Sabo ya ƙara da cewa taron horaswar zai baiwa matasa damar zama jakadu nagari a cikin al’umma musamman a lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Taron horaswar dai ya mayar da hankali ne kacokam akan yadda za a chanza tunanin matasa akan mummunar fahimtar da su ke ita akan cutar korona a jihar Kano.

Dakta Khalid Garba Muhammad na sashen kimiyyar hada magunguna na jami’ar Bayero da ke Kano, ya gabatarwa da matasan wata ƙasida mai taken “Yadda ake gane cutar korona, alamominta da kuma yadda ake bazata tare da hanyoyin dakile ta.

Dakta Khalid Garba ya buƙaci matasan da su yi amfani da kwakwalwarsu wajen bin hanyoyin kariya domin takaita bazuwar cutar a cikin al’umma.

A nasa bangaren Malam Kabiru Danladi Lawanti, wanda malami ne a sashen koyar da aikin jarida na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya buƙaci waɗanda su ka samun horon da su ƙirƙi wani dandali a shafukan sada zumunta tare kuma da bibiyarsu.
Malam Kabiru Danladi su mayar da hankali sosai akan bibiyar kafafe sada zumunta domin ganin abin da ya ke wakana.

A nata bangaren Maryam Ado Haruna wacce ita ce shugabar sashen wayar da kan al’umma tare da binciko guraben aiyukan yi, ta yi tsokaci akan yadda matasan za su rubuta takardar neman aiki tare kuma da tsara jadawalin bayanin karatu wato CV da kuma yadda za a fuskanci ganawa a lokacin da aka je neman aiki.

Babban Daraktan cibiyar ta CITAD Malam Y. Z Ya’u, ya ƙarƙare taron makalar da jan hankalin matsan wajen tsarawa tare da rubuta cikakken jadawali akan wani bincike. Malam Y. Z Ya’u ya ce cibiyar ta CITAD a shirye ta ke wajen bayar da tallafi domin gudanar da wannan bincike.

Hussaini Yunusa daya ne daga cikin wadanda su ka samu horon, ya bayyana cewa kafin ya samu wannan horon shi da abokansa ba su yadda akwai cutar korona ba, amma a yau ya tabbatar da cewa cutar ta korona gaskiya ce.

Ita ma Amina Sani wacce daya ce daga wadanda su ka amfana da horaswar, ta bayyana cewa a baya ba ta yadda da sanya takunkumi baki ba ko kuma bayar da tazara a lokacin taro, amma yanzu ta ga amfani sanya takunkumin baki tare kuma da bayar da tazara a lokacin haduwar jama’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *