Uncategorized

Tattaunawar Da Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al'umma (CITAD) Akan Cutar Korona Tare Da Ismail Bala Garba Malami a Jami'ar Bayero ta Kano Game da Littafin Da Suka Wallafa akan Cutar Wato Corona Blues A Ranar 8 Ga Watan Afrilu, 2021

 

A yau Alhamis Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al'umma CITAD, ta gudanar da wata
tattaunawa akan littafin da cibiyar tare da haÉ—in gwiwar gidauniyar MacArthur da kuma cibiyar Ilimi ta
IIE su ka bayar da tallafi, inda maÉ—aba'ar Whetstone su ka wallafa wannan littafin da ya ke wayar da kan
mutane akan annobar cutar Korona, tare da Isma'ila Bala Garba malami a jami'ar Bayero da ke Kano.

Malam Isma'ila Bala Garba ya bayyana dalilan da ya kai su ga wallafa wannan littafin da ya ke ƙunshe da
waƙoƙin da ke wayar da kan al'umma tare da faɗakar da su akan Cutar Korona.

Haka kuma Malam Isma'ila Bala ya bayyana nasarorin da aka samu wajen wayar da kan al'umma game
da yadda cutar ta Korona ta ke.
Ga yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:

"A madadin Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al'umma CITAD, muna yiwa Malam
@IsmailaBala barka da zuwa wannan shafi da za a tattauna akan littafin Corona Blues da ke wayar da
kan al'umma akan cutar Korona"

"Salam. Sunana Ismail Bala. Ni da abokina Khalid Imam muka wallafa liffafin rubutattan wakoki akan
cutar Korona"

Ali Sabo ya yi tambaya ga Mal. @IsmailaBala kamar haka "shin menene manufar wallafa wannan littafi,
kuma mai ya ja hankalinku har kuka wallafa shi?

Ga amsar da ya bayar "Manufar buga wannan littafin shi ne samar da kafa da marubuta za su wayar da
kan mutane akan cutar Korona. Mun fahinci karancin sahihan bayanai akan cutar Korona. Bugu da kari
akwai labarun karya akan cutar. Shiyasa muka dauki gaburun samar da wakoki akan cutar"

Haka kuma an tambayi Malam Isma'ila Bala akan Ko akwai wani shiri da su Mal @IsmailaBala da sauran
wadanda su ka wallafa wakokin Corona Blues su ke yi na rera wakokin tare da sakasu a gidajen rediyo
domin amfanin wadanda ba su iya karatu da rubutu ba?
Sai Malam Isma'il Bala ya bayar da amsa kamar haka "Akwai wannan yunkurin. Ko jiya anyi wata
tattaunawa aka littafin da wata Jami'a a kasar Poland ta shirya. Nan gaba muna da shirin rera wasu daga
cikin wakokin a gidajen rediyo. In da dama ma zamu wallafasu a cikin CD"

An sake yiwa Malam Isma'il tambaya kamar haka "Kawo yanzu waÉ—annan irin nasararori aka samu wajen
wayar da kan al'umma akan cutar Korona game da wannan littafi na Corona Blues?

Malamin ya bayar da amsa kamar haka "An samu nasarori masu yawa. Da farko, mun kaddamar da
wannan littafin a kwanakin baya. Mutane da yawa sun sami halarta wannan taro. Masana daga
bangarori daban daban sunyi sharhi akan cutar Korona ta mahangar littafi"

Malamin ya ƙara da cewa "Sannna jiya an yi tattaunawa ta musamman akan littafi inda masana daga
karar Poland suka yi sharhi akan wakokin da aka wallafa a cikin littafin"
Haka kuma an sake yiwa Malam Isma'il Bala tambaya aka ko akwai wani shiri da su Mal @IsmailaBala su
ke yi game da wayar da kan jama'a akan allurar rigakafin cutar Korona?
Malamin ya bayar da amsa kamar haka "Akwai shirin wasu jerin tattaunawa akan littafin. Zamu rika
amfani da wannan dama ta jawo hankalin mutane akan alfanun allurar rigakafin cutar Korona"

Kamal Garba ya yi tambaya kamar haka "Ta wace hanya kuke ganin zaku cigaba da yada wadannan
wakoki da kuka yi akan wannan cuta, saboda mutane su fadaka?

"Ta hanyar tattaunawa akan littafin. Muna sa ran masana zasu ci gaba da yin sharhi akan littafin. Bugu
da kari zamu ci gaba da rarraba kwafi kwafi na littafin kyauta domin wayar da kan mutane akan cutar
Korona" In ji Malam Isma'il Bala

Hakazalika an sake tambayar Malam Isma'il akan ta wacce hanya jama'a za su iya kaiwa ga mallakar
wannan littafi na Corona Blues?

"Ana raba wannan littafi kyauta ne. Akwai kwafin littafin a wajen Malam Khalid. Haka na za a iya samun
kwafi a ofis din CITAD" In ji Isma'il Bala

Tattaunawar dai ta gudana a shafin shafin Twitter na Hausa mallakin cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da
cigaban al'umma wato CITAD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *