Cibiyar fasahar zamani da cigaban al’umma mai sun CITAD dake Kano ta guddanar da bincike da kuma wallafa littafin dalilan dayasa hare haren da masu tada kayan baya suka samu nasara akan wassu al’umomi ayayinda kuma suka kasa samun nasara akan wassu.
Da yake tsokaci akan littafin jami’in bincike da sadarwa na cibiyar Malam Hamza Ibrahim Chinade, yace binciken ya gano cewa daga cikin dalilan da su kasa wassu al’umomi kin bada bayanai ga hukumomi sun hada da tsoro da rashin amincewa da kuma rashin tabbas akan illar da zata iya jawo masu idan sun bada irin wadannan bayanai, mai yuwa ma tana iya kasancewa wanda aka baiwa bayanin yana cikin masu tada kayar baya.
Ya cigaba da cewa wani abu da za a iya cewa kusa abun mamaki shine a lokacin da aka fara rikicin Boko Haram, akwai al’umomin da suka baiwa jami’an tsaro bayanai ya zama masu matsalla kuma babban dalili shine rashin yarda.
A jawabinta na kaddamar da littafin Dr. Asabe Sadiya Muhammad, ta jami’ar Gwamnatin jihar Bauchi, ta bayana cewa dalilan wallafa littafin shine domin fahimtan abinda ya jawo da kuma hanyar da za a bi domin hana afkuwar irin haka da kuma hanyar dakilewa idan har hakan ya nemi faruwa.
https://www.voahausa.com/a/3925055.html