Cibiyar fasahar sadarwa da cigaban al’umma (CITAD) da haɗin gwiwa da British Council da kuma Prince’s Trust International (PTI) ta ƙaddamar da fara horar da matasa dabarun kasuwancin zamani wanda ya gudana ranar Asabar a Ni’ima Hotel, Kano
Isah Garba shi ne jami’in shirye-shirye na cibiyar fasahar sadarwa da cigaban al’umma ta CITAD ya bayyana cewa horarwar ta wata biyu ce, Kumal za a horar da matasan dabarun Kasuwarcin zamani ne, kafin kuma a damƙa su a hannun waɗanda za su rika ba su shawarwari na tsawon wata 3 da tunanin cewa su ma za su buɗe wuraren kasuwancinsu don magance matsalar rashin aikin yi a ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa babban burinmu waɗannan matasa, kasuwancinsu ya ɗore, a gefe guda kuma waɗanda suke neman aiki su je su nemi aiki kuma su iya amsa tambayoyi da buƙatun waɗanda su ke so su ɗauke su aiki yayin jarabawar ɗaukar aiki”
Sannan ina kira ga waɗannan matasa da su dage kuma su maida hankali su koyi abinda ya kamata don su ci moriyar abin, su fahimta cewa wasu ne suka ɗauki nauyinsu don su ciyar da rayuwarsu gaba”. Inji Mal. Isah Garba
CITAD dai ta ce a ƙarshen bada horon za su gwada fasahar mahalartan, sannan su fitar da mutum takwas masu ƙwazo a cikinsu a ba su jarin Dubu 250,000 kowannensu, domin su tallafawa kasuwancin.
Kazalika, duk waɗanda suke zuwa za a ba su kuɗin mota da kuma abincin da za su ci.