By Salihu Garba, Nasiru Adamu El-Hikaya.
Wata kungiyar bada shawara akan yada sahihan labaru, mai suna Community Information Technology and Development a turance ta ce jita jita ce makamashin rura fitina a tsakanin al’ummar Nigeria
Mallam Zakari Yau yace, idan an dubi yanar gizo za’a ga ana yada jita jita. Akan kuma dauko hotunan rikicin da aka yi a wasu wuraren ko kuma da ya faru da dadewa a sake sasu kamar yanzu suka faru. Wanda bai sani ba zai dauka ya yi amfani dasu, mutane kuma su yi kokarin daukan fansa. Ya ce suna gargadin mutane kada su dauki wani mataki akan abun da suka gani a yanar gizo ba tare da tantancewa ba.
Tsohon shugaban Miyetti Allah Dodo Oroji na Abuja ya amince da nazarin Zakari Yau. Yana cewa bala’i ake son kawowa kasar inda ake kawo hoto daga wata kasa a ce abun dake faruwa cikin kasar ke nan. Duk wanda aka kashe masa danuwa ko aka lalata masa dukiya zai dauki fansa. Idan aka taba Bafillatani zai kai kara kotu ya nemi hakkinsa. Saboda haka bai kamata mutane suna daukan doka a hannunsu ba.
Haka shi ma shugaban kananan kabilun kudancin Kaduna Mark Amani ya goyi bayan kaucewa yada jita jita. Ya yi ga kira kamfanonin waya da su dinga daukan mataki akan duk wani labarin bogi da wani ke yadawa domin tabbatar da zaman lafiya.