COVID-19

CITAD ta Tallafawa Matasa 31 da Fiye da Naira Miliyan 5 Domin Yaƙi da Cutar COVID-19

Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa ta zamani da ci gaban al`umma (CITAD) ta tallafawa matasa guda 31 da tallafin kuɗi fiya da naira miliyan 5 domin daƙile yaɗuwar cutar korona ko COVID-19 a cikin al’umma.

Jami’in yaɗa labarai na Cibiyar ta CITAD, Ali Sabo, ne ya bayyana haka a jiya litinin a gurin rufe horon da cibiyar ta bayar ga matasan, wanda za su koma cikin al’ummar su domin su yi amfani da abin da su ka koya wajen hana yaɗuwar cutar COVID-19 a cikin al’umma.

Tun da farko cibiyar ta CITAD ta bayar da tallafin ne da hadin gwiwar gidauniyar MacArthur da kuma International Institute of Education.

Ali Sabo ya ce sun baiwa matasa guda 120 horo na musamman, sai dai mutum 31 ne su ka yi nasarar samun tallafin bayan da su ka gabatar da tsari tare da kasafin yadda za su gudanar da aikin da ake buƙatar za su gabatar akan cutar ta COVID-19.

Haka kuma Ali Sabo ya ce za su sanya ido wajen ganin yadda matasan za su yi amfani da tallafin wajen yin abin da aka ba su domin su.

Labarai24 ya tattauna da wasu daga cikin waɗanda su ka amfana da tallafin inda su ka bayyana jin dadinsu tare tabbatar da yin amfani da tallafin a inda ya dace

  • “Babu shakka wannan abin alfahari ne la’akari da yadda aka samu matasa maza da mata da su ka samu horo na musamman akan yaÆ™i da cutar COVID-19, wanda kuma tabbas zamu yi amfani da shi a inda ya dace, domin mun samu horon da zamu je mu yi a cikin al’ummar mu” in ji Gazzali Haruna Ibrahim.

Haka shi ma Salim Sani Shehu ya ce tabbas wannan wani abin koyi ne ga sauran cibiyoyin da su ke rajin yaƙi da yaɗuwar annobar COVID-19.

“Wannan shiri da cibiyar CITAD ta yi ya zama abin misali kuma kwaikwayo ga sauran cbiyoyin da su ke rajin yaƙi da annobar cutar korona, domin tabbas CITAD ta yi rawar gani wajen yi mana horo na musamman tare kuma da bamu tallafin domin yin abin da aka bamu horo akai” in ji Salim Sani Shehu.

Isma’il Abdu Bichi, wanda shi ma daya ne daga cikin waɗanda su ka amfana da tallafin ya ce za su yi amfani da tallafin akan abin da aka buƙace su da yi.

“Mun samu horo akan yaki da bazuwar cutar Corona, kuma tabbas wannan horon ya ƙara mana ilimi akan cutar ta COVID-19, kuma za mu koma unguwannin mu domin ganin mun yi amfani da ilimin da mu ka samu akan cutar ta COVID-19” In ji Isma’il Bichi

Taron dai na tsahon kwanaki goma ne, kuma ya gudana ne a dandalin intanet na Zoom.

A ƙarshe Ali Sabo ya ce yana fatan matasan za su cigaba da yin aiki da abin da su ka koya ko bayan ƙarewar tallafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *