Activities & Projects, Activity-report, Uncategorized

CITAD ta raba kyautar kuɗi ga ɗaliban da su ka yi nasara a gasar kacici – kacici da ta shirya

 

Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma CITAD ta rabawa ɗaliban makarantun Sakandare da su ka yi nasara a gasar kaci – kaci da cibiyar ta shirya akan ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa kyautar kuɗi.

Da ya ke jawabi a gurin taron rabon kuɗin jami’i mai kula da gasar kaci – kacin na cibiyar ta CITAD, Malam Kamilu Isa ya ce makarantun Sakandaren da su ka yi nasarar zuwa matakin farko da kuma na biyu an ba su kuɗi kimanin naira dubu ashirin – ashirin, sai kuma makarantar da ta zo ta uku inda aka ba ta naira dubu goma.

Haka kuma cibiyar ta CITAD ta baiwa ɗaliban da su ka jagoranci makarantunsu da su ka yi nasarar lashe mataki na ɗaya da na biyu an ba su kyautar kuɗi naira dubu ashirin – ashirin sai kuma dalibin da ya zo na uku aka ba shi kyautar naira dubu goma.

Makarantun Sakandaren da su ka yi nasara sun haÉ—a da kwalejin fasaha ta Ungogo wato Government Technical Ungogo, inda ta zo mataki na É—aya, sai kuma Kwalejin kimiyya ta Maitama Sule da ke Gaya ta zo na biyu, da kuma Kwalejin fasaha da ke Kano wato GTC Kano, inda ta zo ta uku.

A nasa ɓangaren shugaban hukumar kula da makarantun Sakandare ta jihar Kano, Dakta Bello Shehu ya jawo hankali malamai da ɗalibai akan amfanin ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa, inda ya ce ya zama wajibi ga malamai da ɗalibai da su rungumi ilimin domin fuskantar ƙalubalen zamani.

Idan za a iya tunawa dai cibiyar ta CITAD dai ta shirya gasar ne a ƙarshen shekarar 2020, inda aka samu makarantu fiye da guda arba’in da su ka halarci gasar.

Taron rabon kuÉ—in ya gudana ne a É—akin taro na hukumar kula da makarantun Sakandare na jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *