Uncategorized

CITAD ga waÉ—anda suka samu horo: Ku yi amfani da abinda ku ka koya

CITAD ga waÉ—anda suka samu horo: Ku yi amfani da abinda ku ka koya
An yi kira ga wadanda suka amfana da bada horo kan kasuwanci a Intanet na tsawon mako biyar da su yi amfani da abinda suka koya don su bunkasa kawunansu.

Babban Daraktan Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa, CITAD, Malam Yahuza Zakari Ya’u ne ya yi kiran lokacin wani bada wani horo kan kasuwanci a Intanet na musamman da CITAD ta shirya wa ‘yan mata da manyan mata su 40 a Gidan Mambayya ranar Laraba, 13 ga watan Maris.

Babban Daraktan, wanda jami’i mai kula da bada horo, Malam Ahmad Abdullahi Yakasai ya wakilta ya shawarci wadanda suka amfana da horon kasuwanci a Intanet ɗin da su yi amfani da abinda aka koya musu.
An koya wadanda suka samu horon dabarun yin fim da tace finafinai, zane a Intanet, kasuwancin Intanet da sauransu.

Malam Ya’u ya bayyana cewa ‘yan mata da manyan mata 6,205 ne suka bukaci a ba su horon, aka zabi mutum 40 daga cikinsu, aka kasa su rukuni biyu aka ba su horo na tsawon makonni biyar.

Ya tunatar da wadanda suka amfana sa’ar da suka yi, yadda suka samu nasarar samun wannan horo duk da dubban mutanen da suka nema.

Daga karshe ya gode wa Ofishin Jaladancin Amurka bisa yadda suka tallafa wa shirin kasuwancin.

Wakilan Hukumomi kamar Babban Bankin Najeriya, CBN, Bankin Masana’antu, Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa, NAFDAC, Hukumar Kula da Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Kasa, SMEDAN sun halarci taron bada horon, sun kuma yi wa wadanda suka suka karbi horon bayanin aikace-aikacensu da kuma yadda za su amfana da su.

Sauran wadanda suka yi nasara a fagen kasuwanci su ma sun halarci taron, sun kuma yi magana da wadanda suka karbi horo bisa irin gogewarsu don karfafa musu guiwa su kafa sana’o’insu na kansu.

An kuma nuna wa wadanda suka samu horon yadda za su yi iya wa harkokin kasuwancinsu rijista da Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rijista ta Kasa, CAC.

Culled from Labarai 24
https://labarai24.com/2019/03/14/citad-ga-wa%C9%97anda-suka-samu-horo-ku-yi-amfani-da-abinda-ku-ka-koya/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *