CITAD in the News, Uncategorized

Cin Hanci da Rashawa ne ke ƙara rura wutar rikici a Najeriya – CITAD

 

Daraktan Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma CITAD, Injinya Yunusa Ya’u ya bayyana cewa cin hanci da rashawa da kuma kalaman ɓatanci ne ƙara rura wutar rikici a Najeriya.

Injiniya Yunusa Ya’u ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a lokacin da ya ke gabatar da wasu littafai da cibiyar ta wallafa. Littattafan da su ka haɗa da The Compromised State: How Corruption Sustains Insecurity in Nigeria” da kuma Context and Content in Hate Speech Discourse in Nigeria”

Littafi na farko ya mayar da hankali ne akan yadda cin hanci da rashawa ke ƙara rura wutar rikicin da ke faruwa a Najeriya, sai kuma na biyun wanda ya mayar da hakali akan illar da kalaman batanci kan haifar a cikin al’umma tare da kawo rashin zaman lafiya.

Daraktan ya ce kalaman ɓatanci da cin hanci da rashawa su ne ke ƙara rura wutar rikici a Najeriya, kuma abu ne mai wahala a samu nasara akan yaƙin da ake da ayyukan ta’addanci muddin ba a yaki wadannan abubuwa ba to abu ne mai wahala a samu zaman lafiya da cigaba.

Injinya Yunusa Ya’u ya ce a dalilin cin hanci da rashawa da ya mamaye ɓangaren tsaron kasar nan ya sanya masu riƙe da shugabancin ɓangaren ke fatan ganin an cigaba da samun rashin kwanciyar hankali domin kawai su dawwama akan mulkin gurin.

Hakazalika, daraktan ya ƙara da cewa bai kamata al’amarin yaƙi da cin hanci da rashawa ya zama aikin gwamnatin tarayya kaɗai ba, ya dace jihohi su kasance suna taka rawa wajen yaƙi da wannan mummunar ɗabi’ar.

A ƙarshe Injiniya Yunusa Ya’u ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da kungiyoyin sa kai da su mayar da hankali waje fito da abubuwan da za su wayar da kan jama’a akan irin haɗarin da tattare da cin da rashawa tun daga tushe tare da buƙatar gwamnati da ta yi amfani da abin da aka rubuta a cikin littattafan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *