CITAD in the News

An Bullo Da Sabuwar Dabarar Magance Satar Shanun Fulani Makiyaya

 

fulani-herdsmen-612x300-300x147

Ganin yadda satar shanu ya addabi al’ummar Fulani da sauran masu kiwo, musamman a Arewacin kasar nan, wasu cibiyoyi da hukumomi, da ma daidaikun mutane sun dukufa wajen samar da hanyoyin da za a bi wajen saukake, ko magance irin wannan annoba da a kullum makiyaya ke zama cikin zullumi. Hanya ta baya-bayan nan, ita ce

wacce wata cibiya mai wayar da kan Fulani game da fasahar zamani wajen magance wannan mummuna abu ta fito da ita.

Bayanin wannan shiri yana kunshe cikin wata tattaunawa da Jami’in yada labaran na wannan cibiya, wato ‘Center For Information And Technology (CFIT)’, Malam Safyanu Lawal Kabo ya yi da manema labarai a Kaduna cikin makon nan a lokacinn da suka gabatar da wani taron bita ga Fulani don ilimintar da su hanyoyin da za su bi na zamani don hana satar shanun.

Jami’in yada labaran ya ci gba da bayyana cewa sun zo Kaduna ne domin gabatar da taron wayar da kai ga al’ummar Fulanin Game da wannan annoba ta satar shanu da ta addabe su a jihohin Arewacin kasar nan. Ya ce ba a Kaduna kawai suka gabatar da irin wannan taron bita ba, “mun je mun yi a Zamfara, mun je mun yi a jihar Bauchi, sannan kuma ga shi mun zo jihar Kaduna,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa suna gabatar da wadannan taruka ne domin wayar da kan Fulani game da hanyoyin da za su bi na zamani wajen kare kansu da dabbobinsu daga miyagu, “muna ilimantar da su hanyoyin da za su bi na fasahar sadarwa wajen yaki da wannan sata ta shanu a dake yi. Sannan kuma muna ilimantar da su ta hanyar wannan taron bita, irin yunkurin da muke yi na tattara irin wadannan matsaloli. Yanzu haka muna kokarin fito da na’urar gano inda aka nufa da shanu bayan an sace su, wato ‘Tracker’, ta yadda duk inda aka shiga da wadannan shanu za a iya ganinsu”.

Ya kuma bayyana cewa ba su kadai ne za su dauki gabarar gabatar da wannan aiki ba, za su hada da duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar, musanmman gwamnati da sauran jami’an tsaro. Kuma suna sane da cewa yanayin satar shanun sun bambanta da na jihohi. Ya ce, yanayin satar shanun Zamfara daban da na Katsina, daban da na Kaduna. “Za mu bayar da hanyoyin amfani da na’urorin zamani, musamman wayar hannu, ta yadda za mu ilimantar da Bafillatani abin da ya kamata ya yi idan an zo satar masa shanu.

Yanzu haka horon da muke bayarwa ke nan, na yadda za su yi amfani da ‘WhatsApp’. Akwai koyarwar da muke yi na yadda za su yi amfani da kananan wayoyi na hannu, ta yadda da zarar ka tura wasu lambobi, to za a iya gane cewa an sace shanu kaza a wuri kaza, kuma an nufi wuri kaza da su. kuma a yanzu haka.

 

Link    http://hausa.leadership.ng/node/9198

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *