Shugaban sashen sadarwa da aikin jarida na jami’ar Bayero da ke Kano, Dakta Nura Ibrahim ya buƙaci matasa da su yi amfani da shafukan sadarwa na zamani da su yi amfani da shafukan wajen ganin shugabanni sun tabbatar da adalci a dukkanin matakai.
Dakta Nura Ibrahim ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da wata lacca akan yadda matasa za su yi amfani da shafukan na sadarwa wajen ganin shugabanni sun tabbatar da adalci a lokacin da su ke jan ragamar al’umma.
Taron lakcar wadda Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma CITAD ta shirya tare da tallafin gidauniyar MacArthur, zai baiwa matasa horar da matasa 500 a faɗin ƙasar nan akan wannan batu.
Malamin jami’ar ya kuma buƙaci matasan da su dinga bambancewa tsakanin labaran ƙarya da kuma sahihan labarai a lokutan da za su wallafa a shafukan su na sadarwa.
Ya ƙara da cewa yanzu lokaci ne da fasahar sadarwa ta ke da matuƙar tasiri a cikin al’umma, saboda haka ya zama wajibi matasa su yi amfani da shafukan sadarwa wajen ganin an samar da shugabanci na gari.
A nasa ɓangaren daraktan cibiyar Nazarin harkokin demokiraɗiya ta Jami’ar Bayero ta Mambayya, Farfesa Isma’il A Zango jan hakalin matasan ya yi wajen kaucewa yaɗa labaran ƙarya da su kan haifar da rudani a cikin al’umma.
Haka kuma Farfesan ya ce muddin matasan su ka yi amfani da sahihan labarai a shafukan su na sadarwa to haƙiƙa zai sanya shugabanni su yi abin da ya kamata.
Taron lakcar dai yana cikin shirin cibiyar ta CITAD na horar da matasa 500 daga sassan ƙasar nan wanda ya samu tallafin gidauniyar MacArthur.