CITAD in the News, Governance and elections, Hate Speech

Ƙungiyar Samar da Fasaha da Cigaban Zamani CITAD Tayi Bikin Ranar Dimukuradiyya

Cibiyar fasaha da cigaban zamani (CITAD) tayi bikin ranar Dimokuradiyya ta duniya kamar Yadda majalissar Ɗinkin duniya ta ware kowacce ranar 15 ga Satumba 2023, domin Gudanar da wannan muki na ranar Dimukuradiyya, kamar Yadda Ali sabo, ya bayyanawa manema labarai.

Tare da yin magana game da muhimmiyar rawar da mata da matasa ke takawa wajen kare dimokuradiyya a yau da kuma nan gaba.

CITAD ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tallafa wa Yara da matasa baki daya a ɓangaran ilimi, Sana’o’i don basu damar tsayawa da ƙafar su ba tare da jiran gwamnati ta samar da guraben aikinyi ba inda hakan zai taimaka wajen bunƙasa zaman takewar al’umma.

Ali Sabo, Yace CITAD tana gudanar da ayyuka da dama na wayar da kan mata da matasa a harkokin siyasa, domin ƙara musu kwarin gwiwar shiga duk wani abu daya shafi siyasa wanda hakan ke taimakawa wajen samun makoma mai kyau.

CITAD tayi kira ga ƴan siyasa da ke samun goyon bayan matasa da mata a wani ɓangare na ranar dimokradiyya ta duniya dasu yaba musu a gwamnatinsu ta hanyar samar da ofisoshi ga matasa domin kashi 61 cikin 100 na ƴan Najeriya Mata da Matasa ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *