CITAD in the News

Shugabancin Ƙasa shirme Ne Ga Matasa, Zurfafa Tunani shi ne Mafita -farfesa IBK

 

Shehin Malami a fannin harshen turanci dake jami’ar Bayero ,farfesa Ibrahim Bello Kano ya ce zurfafa tunani shi ne mafita ga matasa ba wai shugabancin kasa ba.

Ya bayyana hakan ne a yayin gudunar da taron bita ga matasa da cibiyar bincike da fasahar zamani ta CITAD ta ke shiryawa a duk shekara.

Ya ce matasa na bukatar Karin ilimi Wanda ba zuwa jami’a ne kadai ke bada shaidar samun ilimi ba illah zurfafa tunani a duk wani fanni.

Ferfasa IBK,ya Kara da cewa bai yadda da cewa jan ragamar kasar na gun matasa da ba illa sani da Kuma jajircewa shi ke nuna shugabanci inda muka yi la’akari da fahimta ta a kaso 25.

“shugaba kasa shirme na “matashi ya zama mai kwazo, sanin ya kamata, da Kuma mai neman ilimi,domin ko a yanzu ba shugaba Buhari ne ke mulki ba illa hadin gayya ta ko wanne fanni.

Farfesa Ibrahim Bello Kano ya Kara tuna wa matasa muhimmaci ilimi musamman wajen zurfafa tunani da Kuma samu kwarewa a harkokin su na yau da Kullum.

Shugaba Mai lura da al’amuran bitar a Cibiyar bincike da fasahar sadarwa na zamani CITAD Hajiya harira wakili ta ce, CITAD na shirya wanna bitar ne a duk shekara domin zaburar da matasa a kowanne fanni a kasar nan sanin muhimmaci kan su da Kuma kawo mafita a kan abun da ya shige musu duhu,Wanda wannan taron bitar yake kasance wa Karo na 5 a fadin jahar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *