Uncategorized

CITAD ta ƙaddamar da Sabuwar Manhaja Mai Suna ‘Cigiya’ a Shafin Intanet

Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa Da Cigaban Al’umma CITAD ta ƙaddamar da wata sabuwar Manhaja wacce al’umma za su dinga yin amfani da ita wajen binciko kayan da su ka yar da shi ko kuma ya ɓata.

Manhajar mai suna Cigiya za ta taimakawa matafiyan da kayansu ya É“ata da ko kuma kafafen yaÉ—a labarai wajen saka bayanan kayayyakin da su ka É“ace ko kuma aka daÉ—e ana neman masu kayan amma shiru ba a same su.

Da ya ke jawabi a game da Manhajar Injiniya Kamaluddeen Umar wanda shi ne jagoran Injiniyoyin da su ka samar da Manhajar ya bayyana cewa manhajar za ta taimaka ƙwarai da gaske wajen bincikowa waɗanda kayansu su ka ɓata cikin sauƙi.

Injiniya Kamaluddeen Umar ya ƙara da cewa cibiyar ta CITAD ta yi nazari tare ganin dacewar samar da wannan Manhajar ta Cigiya domin sauƙaƙawa al’umma ganin kayansu da ya ɓace.

Haka kuma Injiniya Kamaluddeen ya ce la’akari da jihar Kano a matsayin cibiyar kasuwanci da kuma yadda ake samun ɓatan kayayyaki a tsakankanin matafiya hakan ne ya sanya cibiyar ta CITAD ta yi haɗin gwiwa da ƙungiyoyin motocin sufuri da na babura masu ƙafa uku wato TOAKAN da ƙungiyar ƴan Tasi ta Tsaya Da Ƙafarka, wajen ganin Manhajar ta yi aikin yadda ya kamata.

Manhajar dai ta Cigiya ita ce irinta ta farko da aka samar kuma tana É—auke da wasu alamomi na musamman. Haka kuma ana iya sabunta a dandalin Manhajoji da ke shafin Intanet wato Play Store.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *